<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Da tunawar ƙaunar Mai Ceto.
 Al'ajabi na ke yi.
 Ga Yesu ya sha wulakanci
 Don laifin da ni na yi.

[V2]
 KORUS
 Al'ajabi! Al'ajabi!
 Wannan waƙa sai in yi.
 Al'ajabi! Al'ajabi!
 Mutuwarsa ta cece ni.

[V3]
 2) Dalilin jiƃinsa mai jini
 Da zafin addu'arsa
 Ba domin kansa ya yi ba,
 Sai domin zunubina.
 Korus

[V4]
 3) Mala'ika ya ji tausayinsa,
 Ya zo daga Sama can
 Domin ya ƙarfafa ransa
 A cikin wahalan nan.
 Korus

[V5]
 4) Ya ɗauke zunubai duka,
 Ya maishe su nasa ne.
 Ya kai su can bayan birni,
 Dominsu ya ba da rai.
 Korus

[V6]
 5) A can cikin daraja tasa
 Zan duba Mai Cetona.
 Zan rera waƙa gare shi
 Domin yawan ƙaunarsa.
 Korus</lyrics>
<title>Da Tunawar Ƙaunar Mai Ceto LW103</title>
<hymn_number>103</hymn_number>
</song>